logo

HAUSA

Antonio Guterres ya yi kira da a kara azama wajen yayata bukatar samar da ilimi ga kowa

2021-01-25 11:12:07 CRI

Babban magatakardar MDD Antonio Guterres, ya yi kira ga sassan masu ruwa da tsaki, da su kara azama wajen ganin kowa da kowa ya samu ilimi.

Mr. Guterres wanda ya yi wannan jan hankali ta kafar bidiyo, cikin jawabin da ya gabatar albarkacin ranar ilimi ta duniya a jiya Lahadi, ya jinjinawa juriyar da dalibai, da malamai, da iyaye suka nuna, a gabar da ake fama da tasirin cutar COVID-19, wadda a lokacin da ta kazanta, ta tilasta rufe kusan daukacin makarantu, da cibiyoyin ilimi da jami’o’i.

Jami’in ya ce, duk da cewa yanayin da ake ciki ya haifar da komawa sabbin dabarun koyo da koyarwa, a hannu guda kuma, hakan ya yanke hanzarin sassan al’ummu, da ba su da damar amfani da sabbin hanyoyin neman ilimi na zamani.

Mr. Guterres ya ce, "Dukkanin mu mun ji a jikin mu. Kuma mun san cewa, ilimi shi ke share fagen samun duk wani ci gaba, shi ke sauya fasalin tattalin arziki, yana yakar yanayin rashin jurewa juna, yana taimakawa wajen kare duniyar mu, tare da cimma kudurorin ci gaba mai dorewa."

Don haka a cewar sa, yayin da duniya ke ci gaba da yaki da wannan annoba, kasancewar ilimi hakki ga kowa, kuma moriya ta daukacin al’umma, ya zama wajibi a kare shi, domin dakile mummunar annobar da za ta game ko ina.  (Saminu)

Saminu Alhassan