logo

HAUSA

Shugabannin kasashen duniya za su halarci taron DAVOS

2021-01-25 11:15:33 CRI

A wannan mako, wakilai kimani 2000 daga kamfanoni daban-daban da gwamnatoci da kungiyoyi masu zaman kansu, da kuma shugabanni da kusoshi kasashe 25 sun halarci dandalin WEF, na tattaunawa kan tattalin arzikin duniya karkashin taron DAVOS ta bidiyo. Inda za su tattauna kan yadda za a magance illar da cutar COVID-19 ke jawowa tattalin arzikin duniya, da nanata wajibcin hadin kan kasa da kasa.

Za a kira taron DAVOS na tattaunawa kan ajandar shekarar 2021, daga ranar 25 zuwa 29 ga watan nan, wanda ke da taken “Shekara mai muhimmanci wajen sake amincewa da juna”, wanda zai taimaka wajen tinkarar kalubalolin da ake fuskanta yanzu, wato na allurar rigakafin cutar, da samar da guraben aikin yi da sauyin yanayi.

Duk shekara a kan kira wannan taro a birnin Davos na Swiss, birnin da ya shahara sosai a fannin wasan gudun kankara. Jiya Lahadi an yi bikin kadamar da taron, inda shugaba mai jagorantar dandalin na WEF Klaus Schwab, da shugaban tarayyar Swiss Guy Parmelin suka gabatar da jawabi.

Cikin jawabinsa, Mr. Klaus Schwab ya ce, matakin farko da ya wajaba a aiwatar shi ne farfado da amincewa da juna, saboda haka ya wajaba a kara hadin kan kasa da kasa karo na farko a wannan taro. (Amina Xu)