logo

HAUSA

Sin: Bai kamata kasashe su rika takara kan batun rigakafin COVID-19 ba

2021-01-25 20:24:16 CRI

Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin, Zhao Lijian, ya bayyana cewa, ya kamata kasashe su zabi alluran rigakafin COVID-19 da ta kwanta musu a rai, maimakon yin takara ko yin fito na fito kan wannan batu.

Rahotanni daga kasar Indiya na cewa, nan da ‘yan makonni masu zuwa ne, ake sa ran kasar ta Indiya za ta samarwa kasashen kudancin Asiya miliyoyin rigakafin na COVID-19, matakin da ake ganin kokari ne na rage tasirin kasar Sin.

Kan wannan batu ne, Zhao Lijian, ya ce alluran rigakafin cutar ta COVID-19, abu ne mai muhimmanci ga al’ummar duniya. A don haka, kasar Sin tana fata da ma maraba da karin kasashe su gaggauta samar da rigakafi masu tsaro da kuma inganci, su kuma samarwa kasashe masu tasowa, ta yadda karin mutane za su ci gajiyarsu.(Ibrahim)