logo

HAUSA

Sin ta ba da tabbaci ga tsabtacaccen ruwan sha a kauyuka

2021-01-25 13:56:55 CRI

Rashin tsabtacaccen ruwan sha ya dade yana addabar wasu kauyuka a nan kasar Sin. Amma, yanzu haka Sin ta cimma nasarar samar da isashen tsabtacaccen ruwan sha a dukkannin kauyuka, a matsayin wani matakin kawar da talauci.

Kudancin jihar Xinjiang matakin karshe ne na aiwatar da shirin samar da isashen tsabtacaccen ruwan sha. Ma’aikatar kula da albarkatun ruwa ta kasar Sin ta yi cikakken nazari a gundumomi daban-daban, musamman ma wasu gundumomi dake fama da matukar talauci, ta yadda za a fitar da manufofi da suka dace da halin da ake ciki a wuraren.

Karkashin taimakon kudade da nanufofi, Xinjiang ta aiwatar da ayyuka fiye da guda 400 a wannan fanni a cikin shirin raya tattalin arzikin kasar Sin na shekaru biyar karo na 13, matakin da ya sa aka kai ga warware wannan matsala a jihar. Alkaluma na nuna cewa, yawan kauyuka da suka kai kashi 90% sun samu tsabtacaccen ruwan sha. Ya zuwa karshen shekarar 2020, yawan matalauta da suka samu tsabtacaccen ruwan sha ya kai miliyan 17.1.

A da can, ruwa mai gishiri da daci, matsala ce da ta fi baiwa jama’a a lardin Gansu wahala. Ya zuwa karshen shekarar 2020, an kammala shirye-shiryen samar da tsabtaccen ruwan sha 121 a gundumomi 31 a lardin, matakin da ya amfani mutane dubu 395.

Ban da Xinjiang da Gansu da suka ci moriyar wannan shiri, akwai kuma wasu mazauna kauyuka su fiye da miliyan 270 a nan kasar Sin da suka ci gajiyar wannan manufa. (Amina Xu)