logo

HAUSA

Morocco ta amince da amfani da rigakafin COVID-19 na Sinopharm a matakin gaggawa

2021-01-24 16:38:29 CRI

A ranar 22 ga wata, ma’aikatar kiwon lafiya ta kasar Morocco ta bayar da rahoto cewa, kasar ta amince da yin amfani da rigakafin COVID-19 na Sinopharm na kasar Sin a matakin gaggawa a hukumance.

Rahoton ya ce, hukumar ba da izini ta kasar dake karkashin ma’aikatar kiwon lafiya ta Morocco ta tsaida kudurin ne bayan da ta yi bincike kan alluran rigakafin na COVID-19 mallakar kamfanin hada magunguna na Sinopharm na kasar Sin, inda wa’adin amincewar zai kai watanni 12.

Rahoton ya kara da cewa, za a fara yin allurar rigakafin cutar a hukumance tun daga mako mai zuwa, bisa mataki na farko, za a fara yiwa mutanen da suka fi fuskantar barazanar yaduwar cutar allurar.

Alkaluman kididdigar ma’aikatar kiwon lafiyar kasar Morocco sun nuna cewa, jiya wato ranar 23 ga wata, adadin sabbin mutanen da aka tabbatar sun kamu da cutar COVID-19 a kasar ya kai 950, ya zuwa yanzu gaba daya adadin mutanen da suka harbu da cutar a kasar ya kai 465769, a ciki, 441693 sun warke daga cutar, sai mutane 8128 da suka mutu a sakamakon cutar.(Jamila)