logo

HAUSA

Xinjiang na kokarin kyautata tsarin lafiya domin tabbatar da rayuwar al’ummun yankin

2021-01-24 16:43:37 CRI

A ko da yaushe yankin Xinjiang mai cin gashin kansa na kasar Sin yana maida hankali matuka kan aikin kyautata tsarin kiwon lafiya domin fitar da al’ummun yankin daga kangin talauci ta hanyar daga matsayin hidimomin aikin likitanci.

Xinjiang na kokarin kyautata tsarin lafiya domin tabbatar da rayuwar al’ummun yankin_fororder_1

Cuta mai tsanani kan sake jefa manoma da makiyaya cikin mawuyacin yanayin fama da talauci, a don haka yankin Xinjiang yana ba da muhimmanci sosai kan inshorar cututtuka masu tsanani ga al’ummun yankin dake fama da kangin talauci, sakamakon haka, matalauta kaso 99.97 cikin 100 wadanda suka kamu da cututtuka masu tsanani dake yankin suna iya samun inshorar lafiya.

Xinjiang na kokarin kyautata tsarin lafiya domin tabbatar da rayuwar al’ummun yankin_fororder_2

A cikin ‘yan shekarun da suka gabata, yankin Xinjiang ya kara dukufa kan aikin gina asibitocin garuruwa 900 da asibitocin kauyuka 8600 a fadin yankin, domin kyautata tsarin kiwon lafiya, tare da tabbatar da ingancin rayuwar al’ummun yankin.(Jamila)