logo

HAUSA

Sin za ta gina kamfanonin fasahar 5G guda 30 nan da shekarar 2023

2021-01-24 16:31:23 CRI

Kasar Sin ta himmatu wajen gina cikakkun cibiyoyin fasahar 5G guda 30 da suka shafi manyan sana’o’i 10 nan da shekarar 2023, yayin da kasar ke gaggauta bunkasa kamfanonin intanet ta hanyar amfani da fashohin 5G.

Kamfanonin intanet uku zuwa biyar dake da tasirin kasa da kasa za su fara aiki, kuma za a kafa cibiyar adana manyan bayanan kamfanonin intanet nan da shekarar 2023, kamar yadda shirin tsara bunkasuwar kamfanonin intanet nan da shekaru uku masu zuwa, wanda ma’aikatar masana’antu da fasahohin sadarwa ta kasar Sin MIIT ta bayyana.

A cewar jadawalin shirin, nan da shekaru uku masu zuwa wato  shekarun (2021-2023) shi ne wa’adin gaggauta bunkasuwar kamfanonin intanet na masana’antun kasar Sin. Za a cimma nasarar kafa tsarin masana’antu masu amfani da sabbin fasahohin zamani, gami da amfani da tsarin hadin gwiwa a cikin wannan wa’adin.

Alkaluman MIIT sun bayyana cewa, kasar Sin ta riga ta cimma nasarar kafa manyan dandalloin intanet na masana’antu sama da 70, inda suka hada kayayyakin masana’antu kusan miliyan 60 da kuma kamfanonin masana’antu sama da 400,000.(Ahmad)