logo

HAUSA

Africa CDC ta bukaci kasashen nahiyar su tsaurara matakai yayin da annobar COVID-19 ke kara yaduwa

2021-01-24 15:58:46 CRI

Hukumar dakile cututtuka masu yaduwa ta Afrika CDC, ta gargadi kasashen Afrika da su ci gaba da lura da matakan da suke dauka yayin da ake ci gaba da samun bazuwar annobar COVID-19 a duk fadin nahiyar.

Ya kamata dukkan mambobin kasashen su ci gaba da tsaurara matakan sanya ido da lura domin dakile yadda annobar sarkewar numfashi ta COVID-19 ke ci gaba da ta’azzara, da sanya ido a bangaren zirga zirga, da gano tarihin mutanen da suka yi mu’amala da masu dauke da cutar, da yin gwajin cutar ta COVID-19, da kuma gaggauta sanar da hukumomin lafiya, kamar yadda hukumar kula da lafiyar ta AU ta bayyana cikin gargadin da ta fitar game da halin da ake ciki dangane da cutar ta COVID-19.

Hukumar ta bukaci mambobin kasashen AU da su dinga bin diddigin mutanen da aka tabbatar sun harbu da cutar ta hanyar gano yadda aka yada cutar da kuma yanayin karfin da kasar ke da shi, kana da sanar da bayanai ga hukumomin WHO da Africa CDC game da alkaluman mutanen da ake zato da kuma wadanda aka tabbatar sun kamu da cutar ta COVID-19, da yawan mutanen da suka mutu, da wadanda suka warke, da yawan gwaje gwajen da aka gudanar, kana da yawan jami’an lafiyar da suka harbu da cutar, ya kamata a dinga sanar da wadannan bayanai da sauran bayanan da suka dace a kan lokaci, in ji Afrika CDC.

Ya zuwa yammacin ranar Asabar, adadin mutanen da suka kamu da cutar COVID-19 a nahiyar Afrika ya kai 3,393,591, kana yawan mutanen da cutar ta kashe ya kai 83,859, kamar yadda alkaluman baya bayan nan na Africa CDC suka nuna.(Ahmad)