logo

HAUSA

Alluran rigakafin cutar COVID-19 na kasar Sin na taimakawa kasashe da dama yaki da cutar

2021-01-23 17:00:01 CRI

A baya-bayan nan, wasu kasashe da yankuna sun amince da rajista tare da sayar da alluran rigakafin annobar COVID-19 kirar kasar Sin domin amfanin gaggawa, kuma karin kasashe da yankuna sun cimma yarjejeniyar sayen alluran rigakafin. Alluran rigakafin na kasar Sin na taimakawa wajen bada kwarin gwiwar yakar cutar ga wadannan kasashe da yankuna.

A ranar 19 ga wata, ministan lafiya na kasar Serbia Zlatibor Lončar, ya karbi allurar rigakafin da kamfanin Sinopharm na kasar Sin ya samar, inda ya zama mutum na farko da aka yi wa allurar kirar kasar Sin a kasar Serbia.

Kasar Azerbaijan ma ta kaddamar da mataki na farko na yin alluran rigakafin COVID-19 a hukumance a ranar 18 ga wata. Ministan Lafiya na kasar Ogtay Shiraliyev ne ya jagoranci karbar allurar da kamfanin Sinovac na kasar Sin ya samar.

A nata bangaren, a ranar 20 ga wata, cibiyar nazarin kiwon lafiyar jama'a ta kasar Chile, ta sanar da bada izinin amfani da allurar rigakafin da kamfanin Sinovac ya samar, a matakin gaggawa. A kuma ranar 18 ne, hukumar kula da ingancin magunguna ta kasar Pakistan, ta ba da izini ga kamfanin Sinopharm na Sin, domin amfani da allurar rigakafinsa cikin gaggawa.

A kasar Iraki kuwa, ma’aikatar lafiya ta kasar ta sanar a ranar 19 ga wata cewa, ta amince a yi amfani da alluran rigakafin kasar Sin cikin gaggawa don magance yaduwar annobar COVID-19 a kasar. (Bilkisu)