logo

HAUSA

Nijeriya na jiran tabbacin karshe na samun alluran riga kafin COVID-19 daga shirin COVAX

2021-01-23 15:52:42 CRI

Nijeriya na sa ran samun tabbaci na karshe na samun alluran rigakafin COVID-19, daga shirin kawancen kasashe na samar da alluran rigakafin COVID-19 na COVAX, wanda hukumar lafiya ta duniya ke jagoranta.

Darakta Janar na hukumar raya kiwon lafiya a matakin farko na kasar, Faisal Shuaib, ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na kasar (NAN) cewa, ana sa ran samun kashi na farko na riga kafin a watan Fabreru, inda za a mayar da hankali wajen yi wa jami’an lafiya da manyan jami’an gwmnati da kuma mutane masu rauni.

Faisal Shuaib ya ce kasar na da burin yi wa kaso 70 na al’umarta riga kafin, yana mai cewa kashi na farkon zai isa a yi wa mutane 50,000.

Ya ce za a fara yin alluarar ne ga jami’an lafiya dake aiki a cibiyoyin killace masu cutar da masu taimaka musu da kuma jami’an gwamnati.

Wasu rahotanni daga kafafen yada labaran kasan na cewa, Nijeriya na fatan samun alluran riga kafin COVID-19 miliyan 42 daga shirin COVAX, wanda za a yi 1 bisa 5 na al’ummar kasar. (Fa’iza Mustapha)