logo

HAUSA

Shugaban Guinea Bissau ya kaddamar da ginin babban titin da Sin ta samar da kudin aiwatarwa a kasar

2021-01-23 16:13:04 CRI

Shugaban kasar Guinea Bissau, Umaro Sissoco Embalo, ya jagoranci bikin aza harsashin ginin babban titi mai tsawon kilomita 14 da kasar Sin ta samar da kudin aiwatarwa a kasar, wanda ya hada birnin Bissau da karkarar Safim.

An gudanar da bikin ne jiya, a babban shataletalen filin jirgin saman kasa da kasa na Osvaldo Vieira dake Bissau, inda ya samu halartar jami’an gwamnati da jami’an diflomasiyya dake kasar.

A jawabinsa, shugaba Embalo ya godewa kasar Sin bisa gagarumar gudunmuwar da ta bayar. (Fa’iza Msutapha)