logo

HAUSA

Xi Jinping ya taya takwaransa na kasar Afirka ta tsakiya murna

2021-01-23 15:38:22 CRI

Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya aike da sako ga Faustin-Archange Touadéra, don taya shi murnar lashe zaben shugabancin Jamhuriyar Afirka ta tsakiya.

A cikin sakon, Xi Jinping ya nuna cewa, huldar dake tsakanin Sin da Afirka ta tsakiya ta kasance mai samun kyakkyawan ci gaba a cikin 'yan shekarun nan. Ya kara da cewa, yana ba da muhimmanci ga ci gaban alakar kasashen biyu, kuma yana son hada hannu da shugaba Touadéra don inganta samun karin sakamako ta hanyar hadin gwiwar abota tsakanin bangarorin biyu don amfanawa kasashen da jama'arsu. (Bilkisu)