logo

HAUSA

Zaunannen kwamitin majalisar wakilan jama’ar Sin ya kammala zama na 25

2021-01-23 16:45:31 CRI

Zaunannen kwamitin majalisar wakilan jama’ar kasar Sin karo na 13, ya kammala zamansa na 25, jiya Juma’a a nan Beijing.

Yayin kammala zaman, ‘yan majalisar sun amince da dokar kare annobar dabbobi da ta hukunta keta ka'idojin gwamnati, wadanda aka yi wa gyaran fuska da kuma dokar tsaron gabobin ruwa.

Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya rattaba hannu kan dokokin, wanda ke nufin bada umarnin zartar da su.

Shugaban zaunannen kwamitin, Li Zhanshu ne ya jagoranci zaman, wanda ya samu halartar mambobin kwamitin 160.

Da yake tsokaci kan dokokin, Li Zhanshu, ya ce dokar tsaron gabar ruwan na bada tabbacin shari’a na kare yankuna da tsaron kasa da hakkoki da maradun dake da su a yankunan ruwa yadda ya kamata.

Ita kuwa dokar kare annobar dabbobi, na bayyana kare lafiya da rayukan jama’a da inganta tsarin shari’a na kula da lafiyar dabbobi, yayin da dokar hukunta keta ka'idojin gwamnati ke inganta gina gwamnati karkashin dokoki. (Fa’iza Mustapha)