logo

HAUSA

Xi Jinping ya yi jawabi a cikakken taron shekara-shekara na kwamitin ladabtarwa na kwamitin tsakiyar JKS

2021-01-22 21:07:46 CRI

An gudanar da cikakken taro na shekara-shekara na 2021, na kwamitin ladabtarwa na kwamitin tsakiyar jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin (JKS) a yau Juma’a a nan birnin Beijing. Shugaban kasar Sin, kuma babban sakataren kwamitin tsakiya na jam'iyyar JKS Xi Jinping, ya halarci taron, kana ya gabatar da jawabi.

Taron dai zai yi nazari ne kan ayyukan dubawa, da bincike kan ladabtarwa na wannan shekarar. A yayin taron da ofishin siyasa na kwamitin tsakiya na jam'iyyar ya shirya kafin haka, an bayyana cewa, mai yiwuwa ne za a dora muhimmanci kan zurfafa yin kwaskwarima ga tsarin sanya ido da bincike, da kuma inganta tsarin doka. (Bilkisu)