logo

HAUSA

Jakadan Sin ya bukaci kasashen duniya su taimakawa CAR wajen inganta tsaro da raya ci gaba

2021-01-22 12:49:41 CRI

A jiya Alhamis jakadan kasar Sin ya bukaci kasashen duniya su tallafawa jamhuriyar tsakiyar Afrika CAR, domin inganta yanayin tsaron kasar da kuma bunkasa ci gaban kasar.

Kasar Sin ta bukaci dukkan bangarori masu ruwa da tsaki da su sanya moriyar kasar da bukatun al’ummar kasar sama komai, su girmama matakin karshe da kotun kundin tsarin mulkin kasar ta amince da shi, su mutunta yarjejeniyar zaman lafiyar kasar, su kaucewa tashin hankali, kana su warware dukkan sabani dake tsakaninsu ta hanyar dokokin cikin gidan kasar, in ji jakadan na Sin.

Ya ce, kasar Sin ta jaddada kudirinta na kokarin tabbatar da zaman lafiya da bunkasa ci gaban kasar. Kasar Sin ta samar da taimako gwargwadon karfinta ga CAR domin taimaka mata a yaki da annobar COVID-19 da kuma shirye shiryen gudunar da babban zaben kasar. Kasar Sin za ta yi aiki tare da al’ummar kasa da kasa domin ci gaba da bada gudunmawa wajen tabbatar da zaman lafiya da cigaban jamhuriyar tsakiyar Afrika. (Ahmad Fagam)