logo

HAUSA

Yunkurin kushe Sin game da sanyawa Pompeo da wasu ‘yan siyasar Amurka takunkumi rashin adalci ne

2021-01-22 21:20:43 CRI

Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen Sin Hua Chunying, ta ce yunkurin da Michael McCaul, babban mamban majalissar wakilan Amurka tsagin ‘yan Republican ya yi, na kushe takunkumin da Sin ta kakabawa tsohon sakataren wajen Amurka Mike Pompeo, da sauran wasu ‘yan siyasar kasar rashin adalci ne.

Yayin taron manema labarai da ya gudana a Juma’ar nan, Hua ta soki ra’ayin Mr. McCaul, wanda mamba ne a kwamitin harkokin waje na majalissar wakilan kasar Amurka, tana mai cewa kalaman sa sun dada fito da halayyar Amurka a fili, ta nuna fin karfi da cin zali da danniya, duba da yadda da yawa daga ‘yan siyasar kasar ke goyon bayan muzgunawa sauran kasashe, tare da kokarin hana kasashen su kare kan su.

Wasu rahotanni sun ruwaito Michael McCaul, na bayyana takunkumin da Sin ta kakabawa Mike Pompeo, da sauran wasu ‘yan siyasar kasar a matsayin mataki maras tushe.

Da take amsa tambaya game da hakan, Hua Chunying ta ce Sin ta sanyawa jami’an takunkumi ne, saboda mummunar rawar da suka taka wajen keta hurumin ikon mulkin kai, da tsaro da ci gaban al’amura da suka shafi kasar Sin.

Jami’ar ta ce an dauki dukkanin matakan ne bisa doka kuma sun zama wajibi. Kaza lika sun dada tabbatar da kudurin gwamnatin Sin na kare moriyar kasar.  (Saminu)