logo

HAUSA

Amurka na kara samun wadanda ke mutuwa a rana sakamakon COVID-19

2021-01-22 14:05:46 CRI

Rahotanni daga kasar Amurka na cewa, sama da mutane 4,300 ne suka mutu a duk rana sakamakon cutar COVID-19, a yayin da aka rantsar da sabuwar gwamnati a kasar.

A cewar cibiyar kandagarki da dakile yaduwar cututtuka ta kasar (CDC), an ba da rahoton sabbin mutane 188,156 da suka kamu da cutar, baya ga mutane 4,383 da cutar ta halaka a sassan kasar a ranar Laraba.

Alkaluman cibiyar sun nuna cewa, yanzu haka, a kowace rana, ana samun a kalla mutane 194,000 dake kamuwa da cutar, sai kuma mutane 3,000 da ke mutuwa sanadiyar cutar.

A jiya ne dai shugaban kasar Amurka Joe Biden, ya gabatar da matakansa na yaki da cutar COVID-19, tare da sanya hannu kan karin dokokin shugaba na yaki da annobar. Yana mai cewa, shirin nasa, zai fara ne da “gangamin alluran riga kafin annobar, inda ya kira shirin yiwa ’yan kasar riga kafi a matsayin “wanda bai yi nasara ba” ya zuwa yanzu. (Ibrahim)