logo

HAUSA

An tabbatar da ingancin alluran riga kafin Sinocav na kasar Sin

2021-01-22 12:54:07 CRI

Shugaban kamfanin harhada magungunan Sinovac na kasar Sin Yin Weidong, ya bayyana cewa, sakamakon gwajin da aka yi kan alluran riga kafin COVID-19 da kamfanin Sinovac na kasar Sin ya samar, ya nuna cewa, riga kafin yana da inganci matuka, kuma zai iya yin tasiri kan nau’o’in annobar daban-daban. An dai gudanar da mataki na uku na gwajin allurar ce a kasashen Brazil, da Indonesia, da kuma Turkiya.

Yin ya bayyana yayin wata zantawa da kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewa, sakamakon gwajin da aka gudanar a wadannan kasashe uku, ya ba su tabbaci game da inganci da tsaro na allurar riga kafin. (Ibrahim Yaya)