WHO:Sayen alluran rigakafin COVID-19 fiye da yadda ake bukata da manyan kasashe ke yi ka iya tauye kokarin Afrika na yakar cutar
2021-01-22 11:23:26 CRI
Hukumar lafiya ta duniya WHO, ta ce yakin da nahiyar Afrika ke yi da cutar COVID-19 ka iya fuskantar koma baya, saboda rashin samun isassun alluran riga kafi, sanadiyyar sayewa da manyan kasashe ke yi.
Daraktar hukumar a Afrika, Matshidiso Moeti, ta ce yadda manyan kasashe ke saye alluran riga kafin, ka iya rage damar samunta a nahiyar ta Afirka, sannan zai tauye kokarin da ake na dakile annobar.
Kididdigar hukumar, ta nuna cewa, kawo yanzu, an yi amfani da alluran miliyan 40 a kasashe 50 mafiya arziki, yayin da a nahiyar Afrika, mutane 25 kadai aka yi wa a kasar Guinea. (Fa’iza Mustapha)
Labarai Masu Nasaba
- Alluran riga kafin CNBG na kasar Sin zai yi tasiri a kan nau’o’in COVID-19
- An yaba da matakan da gwamnatin kasar Sin take dauka domin karfafa hadin-gwiwa da sauran kasashe wajen samar da allurar riga-kafin annobar COVID-19
- Babban sakataren WHO ya bukaci a yi wa mutane allurar rigakafi cikin adalci
- Sassa Daban Daban Na Afirka Sun Nuna Karfin Gwiwa Kan Yadda Rigakafin Kasar Sin Zai Taimakawa Nahiyar Wajen Yaki Da Annobar COVID-19