logo

HAUSA

Xi ya jaddada muhimmancin aiki da dokokin jam’iyya a lokacin aiwatar da ajandar raya kasa ta shekaru 5 karo na 14

2021-01-22 22:17:14 CRI

Xi ya jaddada muhimmancin aiki da dokokin jam’iyya a lokacin aiwatar da ajandar raya kasa ta shekaru 5 karo na 14_fororder_微信图片_20210122222152

Shugaban kasar Sin, kuma babban sakataren kwamitin kolin JKS Xi Jinping, ya jaddada muhimmancin dagewa wajen aiwatar da ka’idoji, da kare muradun da aka shimfida karkashin tsarin JKS a dukkanin fannoni, da kaiwa ga cimma nasarar hakan, yayin da ake aiwatar da ajandar ci gaban kasar Sin ta shekaru 5 karo na 14, tsakanin shekarar 2021 zuwa 2025.

Xi ya yi wannan tsokaci ne a yau Juma’a, yayin taro na shekara-shekara na kwamitin ladabtarwar kwamitin kolin jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin.

Xi ya ce, kwamitin kolin JKS ya amince da irin ci gaban da aka samu, a fannin gina tsarin aiwatar da gwamnati mai tsafta, da kuma yaki da cin hanci.Ya ce an kafa babban tarihi, duk da cewa akwai karin kalubale da yanayi mai sarkakiya da ake fuskanta.

Xi ya kara da cewa, za a ci gaba da gwagwarmaya tsakanin cin hanci da matakan yaki da shi a tsawon lokaci. Kaza lika shugaba Xi ya ce, ba wata hanya ta dama ta yaki da cin hanci, wadda ta wuce kara azama wajen kawar da shi, don haka ya zama dole a zage damtse wajen wannan aiki, duk kuwa da irin wahalhalu dake tattare da hakan.  (Saminu)