logo

HAUSA

Adadin wadanda aka tabbatar sun kamu da cutar COVID-19 a Afrika sun zarce miliyan 3.3

2021-01-22 13:52:09 CRI

Cibiyar kandagarki da dakile yaduwar cututtuka ta Africa CDC, ta ce adadin wadanda aka tabbatar sun kamu da cutar COVID-19 a fadin nahiyar, ya kai miliyan 3,337,028

A cewar alkaluman hukumar, yawan wadanda cutar ta kashe a nahiyar ya tsaya kan 81,861.

Bisa rahoton ma’aikatar lafiya ta kasar Habasha, an samu sabbin mutane 292 da suka kamu da cutar cikin sa’o’i 24, wanda ya kawo adadin a kasar zuwa 132,326.

Adadin wadanda cutar ta kashe a kasar kuwa, ya kai 2,057 zuwa yammacin jiya Alhamis, bayan an samu rahoton mutuwar mutane 13.

Hukumar dakile yaduwar cututtuka ta kasar Libya kuma, ta bayar da rahoton samun sabbin mutane 622 da aka tabbatar sun kamu da cutar, wanda ya kawo jimilar adadin a kasar zuwa 111,746.  (Fa’iza Mustapha)