logo

HAUSA

Kenya za ta fito da wasu alkaluman yawon bude ido da za su taimakawa aikin farfadowa bayan annobar COVID-19

2021-01-22 13:01:03 CRI

Babban sakataren ma’aikatan harkokin yawon shakatawa da kare namun daji na kasar Kenya Najib Balala, ya bayyana shirin kasarsa na fito da wasu alkaluman yawon shakatawa da za su kwantar da hankalin jama’a, a wani mataki na taimakawa kasar farfadowa, bayan annobar COVID-19.

Jami’in ya bayyana cewa, harkokin yawon shakatawa da tafiye-tafiye, na daya daga cikin manyan harkokin tattalin arzikin kasar Kenya, wadanda ke ba da gagarumar gudummawa ga kudaden shiga da samar da ayyukan yi, baya ga tasirin da suke da shi ga sauran sassan tattalin arzikin kasar.

Najib Balala ya bayyana cewa, idan har jama’a suka martaba dokokin masana lafiya da matakan kariya na yaki da COVID-19 da aka gindaya, to, sannu a hankali, sashen zai dawo hayyacinsa, har ma ya karfafa sashen tafiye-tafiye na cikin gida.

A don haka, suna fatan cewa, shirin allura rigakafin annobar COVID-19 dake gudana a fadin duniya, zai baiwa masu ziyara damar kara ziyarar kasar sosai. Zai kuma tabbatar da tsaron bangaren na yawon bude ido. (Ibrahim Yaya)