logo

HAUSA

"Hadin kai" da "ba da jinya" da shugaban Amurka ya jaddada a jawabinsa abu ne da dangantakar Sin da Amurka ke bukata

2021-01-21 20:34:47 CRI

Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin, Hua Chunying ta bayyana cewa, a cikin shekaru hudu da suka gabata, wasu tsirarun 'yan siyasan Amurka masu adawa da kasar Sin, sun yi karairayi da yawa, tare da harzuka kiyayya, da rarrabuwa saboda son kai.

Al’ummun kasar Sin da Amurka, sun sha wahala matuka daga wajensu. A jawabinsa na rantsuwar kama aiki, shugaban kasar Amurka Joe Biden ya jaddada "hadin kai" da "ba da jinya", wadanda kuma su ne abubuwan da dangantakar dake tsakanin kasashen biyu ke bukata a yanzu haka.

Madam Hua ta bayyana haka ne, a yayin taron manema labaru da aka shirya a yau Alhamis, game da fatanta kan makomar huldar dake tsakanin kasashen Sin da Amurka. Ta kuma taya Mr. Biden murnar kama aiki, a matsayin shugaban Amurka na 46 tun daga ranar 20 ga watan nan. (Bilkisu)