logo

HAUSA

Pompeo na da hannu wajen ingiza ayyukan ta’addanci

2021-01-21 21:43:20 CRI

Mataimakin ministan watsa bayanai na kwamitin JKS a jihar Xinjiang ta Uygur mai cin gashin kai Xu Guixiang, ya bayyana a yayin taron manema labarai da aka shirya jiya Laraba, cewa tsohon sakataren wajen Amurka Mike Pompeo, ya zamo kanwa uwar gami, wajen ingiza ayyukan ta’adanci.

Xu Guixiang ya bayyana hakan ne, yayin da yake martani game da kalaman Pompeo dake nuna fitar da kungiyar ETIM daga jerin kungiyoyin ta’addanci. Jami’in ya ce sanin kowa ne cewa, ETIM kungiyar ‘yan ta’adda ce da kwamitin tsaron MDD, da sauran hukumomin kasa da kasa suka san da zaman ta.

Xu Guixiang ya kara da cewa, ETIM bangare ne na manyan kungiyoyin ‘yan ta’adda na kasa da kasa, wadda ke zama barazana ba ga kasar Sin kadai ba, har ma ga harkokin tsaron sauran al’ummun kasa da kasa.

Jami’in ya ce Pompeo ya kau da kai daga munanan ayyukan ta’addanci da kungiyar ETIM ke aiwatarwa, yana goyon bayan fitar da kungiyar daga jerin kungiyoyin ‘yan ta’adda. Lallai wannan mummunan tunani na koma baya ya haifar da kalubale, da ma burin Amurka na daidaita al’amura, ya kuma yi kafar ungulu ga manufar kasashen duniya na yin hadin gwiwar yaki da ta’addanci.  (Saminu)