logo

HAUSA

Sin ta taya shugaba Touadéra murnar sake lashe zaben jamhuriyar Afirka ta tsakiya

2021-01-21 20:17:37 CRI

Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Hua Chunying, ta ce Sin na taya shugaban jamhuriyar Afirka ta tsakiya Faustin-Archange Touadéra, murnar lashe zaben kasar sa da ya kammala a kwanan baya.

Hua wadda ta bayyana hakan yayin taron manema labarai a yau Alhamis, ta bayyana jamhuriyar Afirka ta tsakiya a matsayin abokiyar arziki, kuma abokiyar huldar Sin a nahiyar Afirka.

Jami’ar ta kara da cewa, Sin a shirye take, da ta yi aiki da jamhuriyar Afirka ta tsakiya, wajen karfafa kawance, da amincewa da juna, da zurfafa hadin gwiwar cin moriyar juna, tare da daga matsayin dangantakar sassan biyu zuwa mataki na gaba.

Hua ta ce, Sin na ganin cewa, karkashin jagorancin shugaba Touadéra, gwamnatin jamhuriyar Afirka ta tsakiya, da al’ummun kasar, za su cimma sabbin nasarori a hanyar su ta sake gina yanayin zaman lafiya, da bunkasa kasa.  (Saminu)