logo

HAUSA

Ofishin jakadancin Sin dake Zimbabwe ya aike da sakon ta’aziya dangane da mutuwar ministan wajen kasar sanadiyar COVID-19

2021-01-21 09:13:59 CRI

A jiya ne ofishin jakadancin kasar Sin dake Zimbabwe, ya aike da sakon ta’aziya biyo bayan mutuwar ministan harkokin wajen kasar Sibusiso Moyo, wanda annobar COVID-19 ta halaka.

Moyo ya mutu ne a ranar Laraba a wani asibiti dake kasar, inda ya zama minista na uku a gwamnatin kasar da cutar ta halaka, tun lokacin da aka ba da rahoton bullar kwayar cutar a kasar a watan Maris din da ya gabata.

A cikin sakon nasa, ofishin jakadancin na Sin ya nuna damuwa matuka, game da mutuwar Laftana janar S.B Moyo. Sanarwar ta kara da cewa, kasar Sin za ta ci gaba da kasancewa tare da kasar Zimbabwe don ganin bayan wannan annoba, wadda ya zuwa yanzu ta halaka rayukan mutane 825, baya ga wasu 28,675 da suka harbu da cutar a kasar Zimbabwe.(Ibrahim)

Bello