logo

HAUSA

Dakarun Somalia da Amurka sun kashe mayakan al-Shabab 3 a yankin kudancin kasar

2021-01-20 09:34:12 CRI

Dakarun Somalia da Amurka, sun kashe mayakan al-Shabab 3, yayin wasu luguden wuta da jiragen yaki suka yi kan mayakan a yankin kudancin kasar Somalia.

Rundunar sojin Amurka dake aiki a nahiyar Afrika wato (Africom) ta ce, an kai hare-haren kan mayakan dake yankunan Jamaame da Scinnele dake kudancin kasar.

Cikin wata sanarwa, kwamandan dakarun kawance, Dagvin Anderson, ya ce an kai hare-haren ne a wuraren da aka san shugabannin al-Shabab na hada ababen fashewa da bayar da horo da shirya kai hare-hare.

A cewar Dagvin Anderson, babu wani farin hula da ya rasa rai ko ya ji rauni sanadiyyar harin da ke zuwa bayan dakarun kawancen sun matse kaimi wajen kai hare-haren kan kungiyoyin ta’adda dake da alaka da kungiyar al-Qaida, a kasar dake kahon Afrika. (Fa’iza Mustapha)