logo

HAUSA

Hana Wani, Hana kai

2021-01-20 18:04:44 CRI

Hana Wani, Hana kai_fororder_微信图片_20210120160039

A yayin da hankulan al’ummomin duniya ya fara kwanciya, bayan fara amfani da wasu alluran riga kafin COVID-19 da wasu kamfanonin harhada magunguna a sassan duniya suka samar, ciki har da kamfanin harhada magunguna na kasar Sin wato SinoVac, wasu kasashen yamma na kokarin mallake alluran riga kafin don amfanin al’ummominsu kadai,maimakon rabawa daukacin al’ummar duniya.

Baya ga wannan matsala, sai ga wasu alkaluma da cibiyar dakile cututtuka masu yaduwa ta Afirka ta fitar sun nuna cewa, ya zuwa 18 ga watan, sama da mutane miliyan 3 sun harbu da cutar, baya ga sama da mutane 78911 da cutar ta hallaka a nahiyar.

Amma duk da wadannan alkaluma, kasashen nahiyar kamar Najeriya, da Afirka ta kudu, da Masar, suna kokarin yiwa al’ummominsu alluran riga kafin cutar ta hanyoyi daban-daban. A matsayinta na sahihiyar kawa ta kasashen nahiyar, kuma kasar dake sahun gaba wajen nazari da samar da riga kafin annobar, kasar Sin tana kokarin raba riga kafin tsakanin kasashen duniya cikin adalci, kamar yadda babban darektan hukumar lafiya ta WHO, Tedros Adhanom ya bukata.

Hana Wani, Hana kai_fororder_微信图片_20210120160046

Idan ba a manta ba, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya yi alkawari tun farko cewa, da zarar kasar Sin ta kammala nazari da samarwa, sannan aka fara amfani da riga kafin, to, kasashen Afirka ne za su fara cin gajiyar alluran riga kafin. Yanzu haka ma, akwai kasashe kamar Brazil, da Masar da Turkiya da Indonesia da wasu kasashe a yankin Turai da suka fara yiwa shugabanni da jami’an lafiya da ma jama’arsu wannan allura ta kasar Sin.

A baya kasashen yamma sun yi ikirarin yaki da annobar tare da sauran kasashen duniya, amma maganar tasu tamkar, shifcin gizo ne. Don haka, batun Kura ta tsira da na bankinta, ba zai taimaka a kokarin da ake yi na ganin bayan wannan annoba cikin hadin gwiwa ba. Wannan tamkar abin da malam Bahaushe ke cewa ne, Wai Mugunta fitsarin fako.

Wannan ne ma ya sa babban darektan hukumar lafiya ta duniya (WHO) Tedros Adhanom Ghebreyesus ya yi kira ga kasashen duniya da su yi wa al’ummomi allurar rigakafi cikin adalci.

Yanzu haka, akwai wasu karin nau’o’in riga kafi sama da 200 da ake aiki a kansu a sassan duniya, ciki har da sama da 60 da aka fara gwajinsu a kasashen Jamus, da Sin, da Rasha, da Burtaniya da Amurka.

Hanya daya tilo ta magance wannan annoba, ita ce hadin gwiwa, amma mallakar riga kafi ko hana wata kasa ko shiyya ko yanki, ba ita ce mafita ta magance wannan annoba da ta cusa duniya cikin garari ba. (Ibrahim Yaya)