logo

HAUSA

Tawagar jami’an lafiya ta Sin ta duba marasa lafiya sama da 4,000 a Ghana a 2020

2021-01-20 10:04:15 CRI

Tawagar jami’an lafiya ta kasar Sin kashi na 9 dake Ghana, ta kammala aikinta na wa’adin shekara 1 a jiya Talata, inda ta ce ta yi jinyar marasa lafiya sama da 4,000, tare da gudanar da tiyata kimanin 200 a cikin shekarar 2020.

Jagoran tawagar, Shi Yongyong, ya ce dukkan mambobinsa sun jajirce wajen sauke nauyin dake wuyansu a asibitin kawance na Sin da Ghana, duk da annobar COVID-19 da ake ci gaba da fama da ita a kasar.

A cewarsa, tawagar ta taka muhimmiyar rawa wajen yaki da annobar, tare da takwarorinta na Ghana.

Tawagar jami’an lafiyar ta kasar Sin, ta kunshi likitoci daga asibitin gargajiya na kasar Sin na lardin Guangdong, daya daga cikin asibitoci mafi inganci dake amfani da ilimin likitancin gargajiya na kasar.

Shi Yongyong ya kara da cewa, tawagar ta dage wajen amfani da dabarun kiwon lafiya na gargajiya wajen jinyar marasa lafiya a kasar, tare da yayata su ga jami’an lafiya na kasar, lamarin da ya samu karbuwa sosai. (Fa’iza Mustapha)