logo

HAUSA

Guterres ya yi Allah wadai da harin da aka kaiwa ma’aikatan wanzar da zaman lafiya a CAR

2021-01-20 11:17:04 CRI

Babban sakataren MDD Antonio Guterres, ya yi Allah wadai da harin kwanton baunan da ake zargin mayakan CPCC da kaiwa ma’aikatan wanzar da zaman lafiyar majalisar a yankunan Bangassou, Mbomou dake Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya (CAR) a ranar Litinin, harin da ya sabbaba kisan ma’aikacin wanzar da zaman lafiya dan kasar Gabon da kuma Morocco.

Wata sanarwar da Stephane Dujarric, mai magana da yawun babban sakataren na MDD ya fitar, ya bayyana cewa, babban sakataren MDDr ya mika sakonsa na ta’aziyya ga iyalan wadanda harin ya rutsa da su, gwamnatocin kasashen Gabon da Morocco da kuma al’ummominsu.

Guterres ya ce, hare-hare kan ma’aikatan dake aikin tabbatar da zaman lafiya, na iya zama laifin yaki. A don haka ya yi kira ga mahukuntan kasar, da su gudanar da bincike kan hare-haren, tare da gurfanar da wadanda suka aika lamarin a gaban kuliya.(Ibrahim)

Ibrahim Yaya