logo

HAUSA

Rahoton dandalin tattalin arzikin duniya: Kamata ya yi a lura da hadari mai daukar dogon lokaci

2021-01-20 14:15:03 CRI

Dandalin tattalin arzikin duniya mai hedkwata a Geneva ya gabatar da wani rahoto a jiya Talata mai taken “Hadarin da duniya za ta fuskanta a shekarar 2021”, inda ya yi gargadin cewa, cutar COVID-19 ta tsananta gibin dake tsakanin masu kudi da matalauta, kuma watalika za ta kawo babbar illa ga bunkasuwar tattalin arzikin duniya cikin shekaru 3 zuwa 5 masu zuwa, kuma za ta tsananta yanayin siyasa da ake ciki, a shekaru 5 zuwa 10 masu zuwa.

Rahoton ya bayyana cewa, a shekarar 2020, bil Adama ya yi biris da barazanar da hadari mai cin dogon zango zai haifar. Ba kawai rayuka da dama cutar ke halakawa ba, har da jawo baraka ga kasashe da yankuna daban-daban.

Babbar darekatar dandalin Saadia Zahidi ta ce, kamata ya yi a dauki matakan da suka dace yayin da gwamnatoci da kamfanoni da al’ummomi suke kokarin fito daga hadarin cutar, don kafa sabon tsarin tattalin arziki da zaman al’ummar kasa, ta yadda za a kara karfin duniya na tinkarar kalubale da kawar da rashin daidaito da adalci da kuma kyautata lafiyar bil Adama da kiyaye muhallin duniya. (Amina Xu)