logo

HAUSA

Gyara Kayanka Baya Zama Sauke Mu Raba

2021-01-19 16:18:56 CRI

Gyara Kayanka Baya Zama Sauke Mu Raba_fororder_微信图片_20210119161752

Majalisar Dinkin Duniya da Kwamitinta na sulhu, sun yi kakkausar suka kan harin da aka kai wa jami’an shirin wanzar da zaman lafiya na majalisar dake aiki a Mali, ranar Juma’ar da ta gabata, lamarin da ya yi sanadin mutuwar jami’in shirin dan kasar Masar, tare da jikkatar wani guda.

Kamar yadda kullum majalisar Dinkin Duniya ke nanatawa, hari kan jami’an wanzar da zaman lafiya ka iya zama laifin yaki karkashin dokokin kasa da kasa. Abun lura shi ne, jami’an wanzar da zaman lafiya ba su da mummunar manufa, manufar su ita ce gyara da tabbatar da zaman lafiya domin kowa ya rayu cikin kwanciyar hankali. Su ma mutane ne kamar kowa, suna da iyaye da iyalai, amma suka zabi su sadaukar da zama tare da su, domin samar da kwanciyar hankali ga daukacin al’ummar duniya. Sai dai abun takaicin shi ne, maimakon girmama su da mutuntawa da kuma kare su, sai suke zama wadanda suka fi fuskantar bazarana. Burinsu shi ne, su ga jama’a cikin kwanciyar hankali da walwala, domin su ma su koma gida ga nasu iyalan. Sai dai, abun ba haka yake ba a wajen marasa kaunar zaman lafiya, domin daukarsu suke a matsayin abokan gaba, idan suke mayar da akalar fadansu zuwa kan wadanda ke da kyakkyawar manufa.  

Gyara Kayanka Baya Zama Sauke Mu Raba_fororder_微信图片_20210119161758

An kafa shirin MINUSMA ne a shekarar 2013, bayan kungiyoyin ’yan ta’adda sun kwace iko da manyan garuruwan dake arewacin kasar Mali a shekarar 2012. Kuma tun bayan kafuwarsa, an yi ammana cewa, yanayin tsaro a kasar yana ingantuwa, saboda kokarin da shirin ke yi. Amma abun takaici shi ne, jami’an MINUSMA da fararen hula a kasar, na ci gaba da zama mafiya fuskantar barazana. A cewar majalisar Dinkin Duniya ma, shirin wanzar da zaman lafiya na MINUSMA, shi ne ke cikin hadari mafi muni, cikin dukkan shirye-shiryenta na wanzar da zaman lafiya a duniya. Zuwa watan Disamban 2020, jami’an shirin da suka hada da fararen hula da sojoji 231 ne suka rasa rayukansu, kuma daga cikinsu, 134 sun mutu ne sanadiyyar munanan hare-haren da ake kai musu. Baya ga wadancan, wasu jami’ai 358 sun ji mummunan rauni.

Akwai bukatar bangarori masu rikici da su fahimci manufar shirye-shiryen wanzar da zaman lafiya da jami’an dake sadaukar da rayukansu wajen ganin sun rayu cikin kwanciyar hankali. Kuma gyara suke yi ba wai danniya ko mulkin mallaka ba. (Faeza Mustapha)