logo

HAUSA

Hungary ta cimma matsaya game da sayen rigakafin Sinopharm na kasar Sin

2021-01-19 20:14:57 CRI

Gwamnatin Hungary ta cimma matsaya da kamfanin Sinopharm na kasar Sin, game da sayen rigakafin da kamfanin ke samarwa, a matakin baya bayan nan da kasar ke dauka na yaki da cutar COVID-19 a cikin gida, maimakon jiran matakin bai daya na Tarayyar turai.

Tun a ranar Alhamis ne Hungary ta cimma matsaya da Sinopharm, domin samarwa, da gaggauta yi wa ‘yan kasar rigakafin cutar, tare da farfado da tattalin arzikin ta dake cikin mawuyacin hali.

Hungary na iya zama ta daya a kungiyar tarayyar Turai wajen yi wa al’ummarta rigakafin ta kasar Sin, idan har hukumomin da abun ya shafa na kasar suka amince da hakan.

Karkashin dokokin tarayyar Turai, dole ne kasar ta nemi amincewar fara amfani da rigakafin cikin matukar gaggawa, maimakon jiran izini daga hukumar nahiyar mai kula da magunguna ko EMA, wadda ita ce ke bayar da izinin fara amfani da magunguna a nahiyar.  (Saminu)