logo

HAUSA

Kasar Sin: Gwamnatin Trump ce ta haddasa rashin zaman lafiyan shiyya da ake fuskanta

2021-01-15 21:15:01 CRI

Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Zhao Lijian, ya bayyana cewa gwamnatin Trump, tana haddasa rudani da bata dangantaka tsakanin kasashe, domin biyan muradunta.

Zhao wanda ya bayyana hakan yayin taron manema labarai, ya ce gwmnatin Trump ce, ta lalata duk wani zaman lafiya da kwanciyar hankali a shiyyar.

Rahotanni na cewa, a kwanakin nan ne, wasu muhimman takardu game da dabarun Amurka kan kasar Indiya da kasashen wadanda ke yankin fasifik, sun bayyana cewa, ya kamata a rage tasirin kasar Sin a yankin na Indiya da kasashen dake yankin fasifik da raba kan kawaye da abokan huldar Amurka, ta yadda kasashen dake shiyyar, za su rage dogaron tattalin arziki kan kasar Sin, da maye gurbin shawarar ziri daya da hanya daya. Haka kuma, Amurka za ta yi aiki da Indiya da sauran kasashe, don jure matakan kasar Sin dake barazana ga ‘yanci da tsaron sauran kasashe.

Da yake mayar da martani kan tambayar da aka yi masa, Zhao Lijian, ya ce, bayanan da abin ya shafa da aka tabo a cikin muhimman takardun, sun kara bankado muni da, kokarin gwamnatin Trump, na nuna adawa da kasar Sin da kawo zagon kasa ga zaman lafiya da kwanciyar hankali a shiyyar, ta hanyar amfani da, abin da ta kira “dabarun da suka shafi Indiya da kasashen dake yankin fasifik”. Dangane da batun raya alaka da kasashe makwabtanta kuwa, har kullum kasar Sin tana martaba hakkin abokantaka mai kyau, da mutunta da juna da nuna daidaito, kuma a shirye take ta shiga a dama da ita, wajen gina sabon hadin gwiwar kasa da kasa da gina al’umma mai kyakkyawar makoma ga daukacin bil-Adama. Kasar Sin ba ta taba neman yin tasiri ba, kuma ita ba kamar Amurka ba ce da take neman kafa kungiya masu ra’ayi daya .(Ibrahim)