logo

HAUSA

Daraktan WHO ya yabawa Sin da sauran kasashe bisa taimakawa shirin bin diddigin annobar COVID-19

2021-01-14 14:10:27 CRI

Babban daraktan hukumar lafiya ta duniya WHO Tedros Adhanom Ghebreyesus, ya sanar a ranar 11 ga watan Janairu cewa, tawagar kasa da kasa masu bincike game da asalin kwayar cutar numfashi ta COVID-19 za su isa kasar Sin a yau Alhamis 14 ga watan Janairu, ya yabawa dukkan wadanda suka taimaka, wanda suka hada har da kasar Sin, wajen gudanar da aikin bin diddigin asalin kwayar cutar, binciken ba kawai yana da muhimmanci wajen dakile annobar ta COVID - 19 ba ne, har ma zai taimakawa fannin gudanar da tsaron lafiyar al’umma na duniya a nan gaba, kana yana da muhimmanci wajen dakile wasu sabbin cutuka da za su iya barkewa a nan gaba.(Ahmad)