logo

HAUSA

Masanan hukumar lafiya ta duniya za su sauka Wuhan yau

2021-01-14 10:55:33 CRI

Yau Alhamis ranar 14 ga wata, masanan kasa da kasa masu kwarewa a fannin tantance asalin kwayoyin cutar COVID-19 na hukumar lafiya ta duniya WHO, za su isa kasar Sin, don gudanar da aikin hadin gwiwa, na nazarin kimiyya tare da masanan kasar Sin.

Jami’an hukumomin gwamnatin kasar Sin sun bayyana cewa, kasar Sin tana fatan gudanar da hadin gwiwa da hukumar lafiya ta duniya, da masanan kasa da kasa, domin taka rawa wajen neman asalin kwayar cutar.

Jiya Laraba, kakakin watsa labarai na hukumar lafiya ta kasar Sin, kuma mataimakin shugaban sashen yada manufa a hukumar Mi Feng, ya fayyace jadawalin ziyarar masanan kasa da kasa na hukumar lafiya ta duniya a kasar Sin, a taron ganawa da manema labarai, inda ya bayyana cewa, “Masanan kasa da kasa na hukumar lafiya ta duniya, za su sauka a birnin Wuhan na lardin Hubei dake nan kasar Sin yau Alhamis ranar 14 ga wata, bisa ka’idar kandagarkin annobar COVID-19 ta kasar Sin, masanan za su killace kansu, yayin da masanan kasar Sin da abin ya shafa za su tattaunawa da su ta kafar bidiyo.”

A ‘yan kwanakin da suka gabata, mataimakin darektan hukumar lafiya ta kasar Sin wanda ke kula da aikin nazarin allurar rigakafin cutar COVID-19, na kungiyar kandagarkin cutar ta majalisar gudanarwar kasar Zeng Yixin, ya taba bayyana cewa, har kullum kasar Sin tana mai da hankali matuka kan aikin gano asalin kwayar cutar, kuma masanan kasar da abin ya shafa sun riga sun yi aiki da yawan gaske, kuma kasar Sin tana goyon bayan masanan kasa da kasa na hukumar lafiya ta duniya, da su gudanar da hadin gwiwar nazarin kimiyya da masanan kasar Sin a birnin Wuhan, yana mai cewa, “Masanan kasa da kasa na hukumar lafiya ta duniya, za su gudanar da hadin gwiwar nazarin kimiyya da masanan kasar Sin a birnin Wuhan, ko shakka babu muna goyon bayan aikin. Hakika kafin wannan, mun riga mun kira taro ta kafar bidiyo har sau hudu, inda muka tattauna da masanan hukumar lafiya ta duniya WHO, game da hakinanin shirin yin nazari, kuma mun cimma matsaya guda. Yanzu haka mun aika tawagar masanan da abun ya shafa, wadanda ke kunshe da masana dake nazarin kwayar cutar, da masana a fannin nazarin ilmomin hana yaduwar cututtuka, da masanan nazarin ilmomin kiwon lafiyar jama’a, da kuma likitocin dake aiki a asibitoci, domin gudanar da hadin gwiwa da masanan kasa da kasa.”

Zeng Yixin ya kara da cewa, gwamnatin kasar Sin tana mai da hankali kan aikin matuka, kuma za ta goyi bayan rangadin aiki na hukumar lafiya ta duniya, da hadin gwiwar nazarin kimiyya dake tsakanin sassan biyu ba tare da rufa rufa ba, yana mai cewa, “A takaice dai, muna iya cewa, muna goyon bayan rangadin aiki na hukumar lafiya ta duniya, da hadin gwiwar nazarin kimiyya tsakanin sassan biyu ba tare da rufa rufa ba, kuma muna fatan hadin gwiwar zai samar da karin taimako gare mu, kana muna cike da imanin cewa, za mu samu sabon sakamako wajen tantance kwayar cutar COVID-19, ta hanyar gudanar da nazarin kimiyya bisa tushen kimiyya, a don haka muna son yin kokari tare da masanan kasa da kasa, domin samun ci gaba a bangaren nazarin kwayar cutar, saboda lamarin yana da babbar ma’ana gare mu, yayin da muke kokarin kandagarkin cututtukan da za su barke ba zato ba tsamani a nan gaba.”

Kafin wannan, kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Zhao Lijian, shi ma ya taba bayyana cewa, tun bayan barkewar annobar COVID-19, a ko da yaushe, kasar Sin tana gudanar da cudanya da hadin gwiwa dake tsakaninta da hukumar lafiya ta duniya wajen samun asalin kwayar cutar. A watan Fabrairu da watan Yulin bara, kasar Sin ta taba gayyatar masanan hukumar lafiya ta duniya har sau biyu, domin su zo nan kasar Sin yin nazari, duk da cewa, a wancan lokaci, kasar Sin ta sha aiki matuka wajen kandagarkin cutar. A sakamakon haka, hukumar lafiya ta duniya, da masanan kasa da kasa da abin ya shafa, sun jinjinawa sakamakon da kasar Sin ta samu wajen hana yaduwar annobar, da kuma tantance asalin kwayar cutar. Kuma har sassan biyu sun riga sun cimma matsaya guda kan aikin gano asalin kwayar cutar, yana mai cewa, “Tantance asalin kwayar cutar COVID-19, banu ne da ya shafi kimiyya, ya dace masanan kasashen duniya su yi aikin cikin hadin gwiwa, kuma kila ne asalin kwayar cutar ya shafi wurare daban daban a fadin duniya, sakamakon sauye-sauyen yanayin yaduwar cutar, da kuma zurfin fahimtar bil Adama game da kwayar cutar, a don haka, kamata ya yi hukumar lafiya ta duniya ta gudanar da rangadin aiki makamancin wannan, a sauran wuraren kasashen duniya. A hannu guda, kasar Sin na fatan gudanar da hadin gwiwa da WHO, da sauran masanan kasa da kasa, ta yadda za ta taka rawar gani, afannin gano asalin kwayar cutar.”(Jamila)