logo

HAUSA

Xi Jinping ya amsa wasikar shugaban musamman na Starbucks

2021-01-14 14:04:48 CRI

Kwanakin baya, shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya amsa wasikar da shugaban musamman na kamfanin Starbucks na Amurka, Howard Schults ya aika masa.

A cikin wasikar, Xi ya nuna cewa, Sin tana wani kokari na gina kasa mai tsarin gurguzu na zamani daga dukkan fannoni, wadda za ta samar da damammaki masu kyau ga bunkasuwar kamfanonin ketare ciki hadda Starbucks. Kuma ya yi imanin Howard Schults da kamfaninsa, za su ci gaba da taka kyakkyawar rawa wajen ingiza hadin gwiwar kasashen Sin da Amurka ta fuskar tattalin arziki da ciniki da raya dangantakar kasashen biyu. (Amina Xu)