logo

HAUSA

Kasar Sin ta fitar da abin rufe baki da fuska sama da biliyan 224 don taimakawa kasashen duniya yaki da COVID-19

2021-01-14 19:36:07 CRI

Rahotanni daga kasar Sin na nuna cewa, daga watan Maris zuwa karshen watan Disamban shekarar 2020, kasar ta fitar da sama da abin rufe baki da fuska biliyan 224.2, a kokarin taimakawa kasashen duniya yakar annobar COVID-19.

Babbar hukumar kwatam ta kasar Sin (GAC) ta bayyana cewa, daga cikin abin rufe baki da fuskan da kasar ta Sin ta fitar zuwa kasashen duniya, biliyan 65 daga cikinsu, na amfanin jami’an lafiya ne. (Ibrahim)