logo

HAUSA

Birtaniya ta samu adadi mafi yawa na wadanda COVID-19 ta hallaka tun farkon barkewarta kawo yanzu

2021-01-14 11:31:41 CRI

Wasu alkaluma da hukumomi a Birtaniya suka fitar a jiya Laraba, sun nuna cewa, adadin mutanen da cutar COVID-19 ta hallaka tun bayan da aka gano kwayar cutar a jikinsu cikin kwanaki 28 da suka gabata sun kai mutum 1,564, adadin da shi ne mafi yawa da kasar ta taba samu a rana guda tun farkon barkewar ta.

Yanzu haka dai adadin wadanda suka rasu, sakamakon harbuwa da cutar ta COVID-19 a Birtaniya, sun kai mutum 84,767, baya ga karin mutane 47,525 da aka tabbatar sun harbu da cutar. Wadannan alkaluma dai sun nuna cewa, jimillar adadi wadanda suka harbu da cutar a Birtaniya sun kai mutum 3,211,576 gaba daya.

Firaministan Birtaniya Boris Johnson, ya sake nanata kira ga al’ummar kasar, da su martaba dokokin kulle da aka sanya, wadanda ke bukatar ‘yan kasar su zauna a gida, ba fita sai dai inda akwai wata bukata ta wajibi. (Saminu)