logo

HAUSA

Kasar Sin ta bukaci bangarorin kasar Mali su cimma matsaya game da gina hukumomi da shirya zabe

2021-01-14 10:35:59 CRI

Mataimakin zaunannen wakilin Sin a MDD Dai Bing, ya yi kira ga dukkan bangarorin kasar Mali, su cimma matsaya guda kan gina hukumomi da shirya zabe.

Ya ce ya kamata dukkan bangarori, su sanya muradun kasar da al’ummarta gaba da komai, su yi amfani da wannan dama ta muhimmiyar gaba da suke kai, su cimma matsaya game da gina hukumomi da shirya zabe, da nufin shimfida tubali mai kwari ga babban zaben da za a yi a badi, da kuma ci gaban kasar.

Dai Bing, ya yi kira da a yi kokarin ci gaba da yaki da ta’addanci, yana mai cewa, Sin na mara baya ga ayyukan shirin MDD dake wanzar da zaman lafiya a kasar, na taimakawa dakarun kawance na kasashen yankin Sahel, kuma ta na goyon bayan gwamnatin rikon kasar, ta ci gaba da shiga ana damawa da ita a kokarin da kasashen yankin Sahel ke yi na yaki da ta’addanci. (Fa’iza Mustapha)