logo

HAUSA

Jami’in MDD ya bukaci a gudanar da sahihin zabe cikin lumana a Uganda

2021-01-14 09:51:45 CRI

Babban sakataren MDD Antonio Guterres, ya bukaci a gudanar da cikakken zabe, mai inganci kuma cikin kwanciyar hankali a kasar Uganda, yayin da ake bude rumfunan zaben kasar a yau.

An dai shirya gudanar da zaben shugaban kasar da na ‘yan majalisar dokokin kasar a yau Alhamis.

Daya daga cikin shugaban kasa mafi jimawa a karagar mulki a Afrika, Yoweri Museveni, yana neman wa’adin shugabancin kasar a karo na shida, kuma zai fafata ne da ‘yan takara 10 a zaben, domin neman cigaba da zama a kujerar shugabancin kasar, daga cikin ‘yan takarar neman shugabancin kasar ta Uganda har da wani shahararren mawakin kasar Bobi Wine.(Ahmad)