logo

HAUSA

MDD ta damu game da masu bukatar agaji a yankunan karkarar Tigray

2021-01-14 09:56:38 CRI

Hukumar kula da ayyukan jin kan bil adama ta MDD ta bayyana matukar damuwa game da dubban daruruwan masu bukatar agaji a yankin Tigray na kasar Habasha, wanda aka kiyasata adadin mutanen dake bukatar agajin domin ceto rayuwarsu ya kai miliyan 2.3.

Ofishin kula da ayyukan jin kai na MDDr OCHA, yace, MDD da abokan huldar dake samar da tallafin jin kan bil adama a Habasha sun yi kiran gaggawa ga dukkan bangarorin da abin ya shafa da su bayar da dama ga jami’an agajin don shigar da kayayyakin tallafin jin kan bil adama ga yankin na Tigray domin tallafawa mutanen dake cikin matsananciyar bukatar tallafin.(Ahmad)