logo

HAUSA

Kasar Sin ta gabatar da wani samfurin jirgin kasa mai matukar sauri

2021-01-14 09:44:29 CRI

Kasar Sin ta gabatar da wani samfurin jirgin kasa mai matukar sauri_fororder_1126979212_16105323742021n

Kasar Sin ta gabatar da wani samfurin jirgin kasa mai matukar sauri_fororder_1126979212_16105323742341n

Kasar Sin ta gabatar da wani samfurin jirgin kasa mai matukar sauri, wanda ke amfani da fasahar zamani ta maganadisu dake iya jure yanayi mai tsanani, a jiya Laraba a birnin Chengdu na kudu maso yammacin kasar.

A cewar jami’ar Jiaotong ta kudu masu yammacin kasar Sin, kuma daya daga cikin wadanda suka fasalta jirgin, an tsara jirgin kirar cikin gida ne ta yadda zai yi gudun kilomita 620 a kowacce sa’a.

Har ila yau a jiyan, an kaddamar da wani layin dogo mai tsawon mita 165 domin gwajin sabon jirgin. (Fa’iza Mustapha)