logo

HAUSA

Ababen more rayuwa da Sin ta gina za su ingiza ci gaban tattalin arzikin gabashin Afrika a 2021

2021-01-14 10:59:22 CRI

Ana sa ran ababen more rayuwa da Sin ta gina, za su ingiza ci gaban tattalin arzikin yankin gabashin Afrika a bana.

Wani manazarci, Judd Murigi, kuma shugaban sashen bincike na kamfanin ICEA LION Asset mai kula da hannayen jari, ya bayyana yayin wani taron kamfanin da aka yi jiya a Nairobin Kenya cewa, ana sa ran bangarorin cinikayya da na sufuri su amfana daga ingantattun ayyukan more rayuwa da Sin ta yi, tare da jagorantar farfadowar tattalin arzikin yankin a bana.

Ya ce kasashen gabashin Afrika na da juriya, saboda yadda suke baza komar tattalin arziki da kuma rashin dogaro kan kayayyakin da suke fitarwa. (Fa’iza Mustapha)