logo

HAUSA

Manazartan duniya sun kirkiro hanyar inganta tiyatar haihuwa a Afrika

2021-01-13 10:52:23 CRI

Wasu manazarta na duniya, sun sanar da kirkiro sabuwar fasahar inganta tiyatar haihuwa a nahiyar Afrika, da nufin bunkasa lafiyar mata masu juna biyu.

Tawagar jami’an lafiya manazartan, ta yi bayanin ta kafar bidiyo cewa, za a kaddamar da sabuwar fasahar tiyatar haihuwar a kasashen Habasha da Liberia da Afrika ta kudu, a wani yunkuri na rage mace-macen mata masu juna biyu da jarirai.

A cewar Jody Lori, daya daga cikin manazartan, kuma ungozoma, fatansu shi ne, kara samar da damar tiyatar haihuwa ga matan da nakuda ta zo musu da matsala, zai inganta lafiyar mata masu juna biyu a Afrika.

Hukumar lafiya ta duniya ta ba da shawarar gudanar da tiyata ga kaso 15 bisa dari na haihuwa da ake yi a cikin kowacce al’umma, domin rage barazana ga iyaye da jariransu.

Tanya Doherty, wata ungozoma a Afrika ta kudu, ta ce wani bangare na kaso 6 bisa dari na mata a yankin kudu da hamadar Sahara ne ke samun haihuwa ta hanyar tiyata, saboda talauci da rashin zuba jari a fannin samar da kayayyakin kiwon lafiya na zamani da kuma al’adu. (Fa’iza Mustapha)