logo

HAUSA

Yawan alluran riga kafin COVID-19 da aka yi wa mutane ya haura miliyan 10 a kasar Sin

2021-01-13 19:37:30 CRI

Yawan alluran riga kafin COVID-19 da aka yi wa mutane ya haura miliyan 10 a kasar Sin_fororder_12

Kwamitin hadin gwiwa na yaki da annobar COVID-19 na majalisar gudanarwar kasar Sin, ya kira wani taron manema labarai da yammacin Larabar nan, inda ya gabatar da sabbin matakansa na kandagarki da yaki da ma jinyar masu fama da annobar COVID-19. Inda ya bayyana cewa, tun lokacin da aka fara aiwatar da aikin riga kafi ga wasu muhimman rukunin al’umma a ranar 15 ga watan Disamban shekarar da ta gabata, yawan alluran riga kafin COVID-19 da aka yi wa mutane ya haura miliyan 10.

Bugu da kari rahotanni na cewa, alluran riga kafin da wani kamfanin kasar Sin ya samar, ya shiga matakin gwaji na uku a kasashen Brazil, da Turkiya, da Indonesia, da Chile. Kuma daga ciki, wanda ya yi tasiri a kasar Turkiya, ya kai kaso 91.25 cikin 100.(Ibrahim)