logo

HAUSA

Demokradiyya ita ce hanya ta dindindin ta shawarwari da tuntuba

2021-01-13 09:56:50 CRI

Babban jami’in MDD a yankin yammacin Afrika Mohamed Ibn Chambas, ya shaidawa kwamitin sulhu na majalisar cewa, zabuka abu ne da ake gudanarwa a wani lokaci guda, yayin da demokradiyya ke zaman hanya ta dindindin, ta shawarwari da tuntubar juna.

Dangane da yanayin zabukan shugaban kasa 5 da na majalisun dokoki 3 da na kananan hukumomi 2 da aka yi a yankin a watannin baya-bayan nan, wakilin na musamman, kuma shugaban ofishin MDD a yankin Sahel da yammacin Afrika (UNOWAS), ya shaidawa kwamitin cewa, hukumomin zabe sun nuna matukar kwarewa wajen shiryawa da gudanar da zabuka.

Da yake gabatar da sabon rahoto kan yankin Sahel da yamacin Afrika, Mohamed ibn Chambas, ya yi bayyani kan zaben shugaban kasar Burkina Faso, yana mai cewa, shawarwari tsakanin masu ruwa da tsaki kan harkar siyasa, ya kai ga daukacinsu sun amince da sakamakon zaben, inda wadanda suka sha kayi suka taya shugaba Roch Marc Christian Kabore, murnar lashe zabe a wa’adi na biyu, inda kuma suka bayyana kudurinsu na hada hannu tare domin magance matsalar tsaro.

Ya kara da cewa, a Ghana, an gudanar da zabukan ba tare da rikici ba, yana mai yabawa gudanar zabe lami lafiya a kasar Niger a ranar 27 ga watan Nuwamban bara, lamarin da ya ce zai ba kasar damar mika mulki karo na farko karkashin tsarin demokradiyya, wato tsakanin zababbun shugabanni.

Dangane da kalubale da dama da aka fuskanta saboda barkewar annobar COVID-19, Ibn Chambas ya ce galibin kasashen yankin sun shiga matsalar tattalin arziki, sannan an sauya akalar amfani da albarkatu, daga sarrafa su zuwa yaki da rashin tsaro.

Yayin da ake rabon allurar rigakafi a lokacin da yankin ke fuskantar yaduwar cutar COVID-19 a karo na biyu, ya ce abu mafi muhimmanci shi ne hada hannu domin aiki da darrusan da aka koya ta fuskar inganta shugabanci da hidimtawa jama’a, domin yankin ya mai juriya da aminci. (Fa’iza Mustapha)