logo

HAUSA

Shugaban Malawi ya ayyana dokar ta baci sakamakon karuwar bazuwar COVID-19

2021-01-13 10:55:25 CRI

Shugaban Malawi ya ayyana dokar ta baci sakamakon karuwar bazuwar COVID-19_fororder_Saminu 2-hoto

Shugaban kasar Malawi Lazarus Chakwera, ya ayyana dokar ta baci a daukacin gundumomin kasar 28, sakamakon karuwar masu harbuwa da cutar COVID-19. Rahotanni na cewa, daga ranar 1 ga watan nan na Janairu, an samu karin sama da mutane 2,000 da suka harbu da cutar, baya ga a kalla mutane 50 da ta hallaka.

Shugaba Chakwera ya bayyana a ranar Talata, yayin wani jawabin musamman da ya gabatar, bayan da cutar ta hallaka ministocin kasar 2 cewa, ayyana dokar ta bacin, shi ne matakin farko, kafin aiwatar da karin matakai, bayan kwamitin majalissar dokokin kasar na tsaro ya amince da su.

Chakwera ya bayyana rasuwar ministan sufuri Muhamad Sidik Mia, da na kula da kananan hukumomi Lingson Berekanyama, a matsayin babbar asara ga kasar.

Tuni dai shugaban na Malawi ya ayyana ranekun 12 zuwa 14 ga watan nan, a matsayin ranekun makoki, inda aka sassauto da tutar kasar a dukkanin wurare zuwa rabin sanda, don girmama manyan jami’an gwamnatin kasar da COVID-19 ta hallaka.

Kaza lika shugaba Chekwera, ya umarci ma’aikatun lafiya, da na kula da tsaron cikin gida, da na Ilimi, da na wayar da kan al’umma, da na kananan hukumomi da shari’a, da su yi aiki tare da mataimakin shugaban kasar Saulos Chilima, don yiwa tsarin kasar na yaki da wannan cuta kwaskwarima. (Saminu)