logo

HAUSA

An bukaci kasashen Afirka da su inganta tsaron yanar gizo domin ba da kariya ga cinikayyar intanet

2021-01-13 09:53:01 CRI

An bukaci kasashen Afirka da su inganta tsaron yanar gizo domin ba da kariya ga cinikayyar intanet_fororder_Saminu1-hoto

Babban jami’in kamfanin Sokoni mai hada hadar sayar da hajoji ta yanar gizo a kasar Kenya Mr. Ebrima Fatty, ya yi kira ga mahukuntan kasashen Afirka, da su dauki matakan samar da isasshiyar kariya ga kafofin yanar gizo, don kyautata cin gajiya daga harkokin cinikayyar zamani, a gabar da kasashen nahiyar ke fuskantar karin barazana daga masu kutse a yanar gizo.

Mr. Fatty, wanda ya yi kiran a jiya Talata yayin ganawa da ’yan jarida, ya ce duba da yadda hajojin latironi, da na amfanin yau da kullum, da kayan kawa ke samun karin karbuwa a nahiyar, tare da kara kyautata rayuwar al’ummar nahiyar, ya dace a baiwa fannin na tsaron intanet kulawar da ta dace.

Jami’in wanda ya bayyana hakan ga manema labarai a birnin Nairobin kasar Kenya, ya kara da cewa, barkewar cutar COVID-19, ta tilasawa masu sayayya rungumar kafar yanar gizo don yin sayayya, musamman a gabar da kasashen suka fara sanya dokokin kulle, don dakile yaduwar annobar.

Ya kara da cewa, a lokacin na kulle, masu dandalin sayayya ta yanar gizo sun samu riba mai tarin yawa, kuma kasuwar su ta kara habaka har zuwa shekarar bana. Don haka a ganinsa, akwai bukatar bullo da dabarun inganta kirkire-kirkire a wannan fanni, ta yadda za ta samu karin bunkasar tattalin arziki, da raga fatara tsakanin al’ummun nahiyar ta Afirka. (Saminu Hassan)