logo

HAUSA

Afirka ta kudu ta rufe kan iyakokinta na tudu don dakile yaduwar COVID-19

2021-01-12 13:34:52 CRI

Shugaban kasar Afirka ta kudu Cyril Ramaphosa, ya sanar da rufe kan iyakokin kasarsa na tudu, har zuwa ranar 15 ga watan Fabarairu mai zuwa, a wani mataki na dakile kara yaduwar cutar COVID-19.

Mr. Ramaphosa ya gabatar da umarnin ne a jiya Litinin, yayin da yake jawabi ga ‘yan kasar, game da yanayin da ake ciki don gane da yaki da wannan cuta. Ya ce, "Domin rage cunkoson al’umma, da yiwuwar kara yaduwar cutar COVID-19, majalissar zartaswar Afirka ta kudu ta amince da rufe tashohin tudu 20 na shiga kasar, har zuwa ranar 15 ga watan Fabarairu, lokacin da ake sa ran sake bude zirga zirga ta tashoshin".

Cikin tashoshin da aka rufe har da ta Beitbridge mai karbar dumbin jama’a, wadda kuma ke kan iyakar kasar da Zimbabwe, da ta Lebombo dake hada kasar da Mozambique, da ta gadar Maseru, dake kan iyakar kasar da Lesotho. Sai kuma ta Oshoek da ta hada kasar da Eswatini.

Shugaba Ramaphosa, ya kara da cewa, za a ba da damar sufurin makamashin mai, da na manyan sundukan hajoji, da sauran kayan bukatar yau da kullum, baya ga harkokin da suka shafi kula da lafiya na gaggawa, ga wadanda ke fuskantar cututtuka masu iya salwantar da rayuwa.    (Saminu)